Website na bugi
Tayaya zaka gane website na gaskiya da kuma na damfara
Wannan website zai baku damar tantance aya da tsakuwa kasancewar a wannnan lokaci ana kirkirar hanyoyi daban-daban na damfara da kuma satarwa mutane bayane domin yi musu illa a lalitarsu ta banki,hakan na faruwane wajan kwadaitar da mutum don ya shiga wannan link da nufin zai samu wata biyan bukata musamman samun kudi (fishing).
Ga link na website din:Shiga nan
Kai tsaye zaka shiga wannan webiste, bayan ka shiga sai ka rubuta sunan website din da kake so a duba maka ko kuma ka dakko link dinsa, daga nan wannan website din zai fada maka komai akan sa.
Wannan website din bashi da wahalararwa wajen amfani dashi, na tabbata da zakuji dadin aiki dashi (zai burge ku).


Comments
Post a Comment